Wasu matasa ƴan majalisa a Majalisar Wakilai sun bukaci Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya sauke Ministan Tsaro, Mohammed Badaru Abubakar, bisa abinda suka kira gaza magance matsalar tsaro da ke kara ta’azzara a Najeriya.
Kungiyar Afenifere Youth Vanguard for Peace in Nigeria (AYPN) ta goyi bayan dan majalisar wakilai daga Jihar Filato, Hon. Yusuf Gagdi, wanda a makon da ya gabata ya bayyana rashin gamsuwarsa da irin yadda Ministan ke tafiyar da sha’anin tsaro a kasar.
Gagdi ya bayyana cewa ‘yan ta’adda sun kai hari a wasu sansanonin sojoji a Borno, inda suka kwace makamai da wasu motocin yaki da aka kiyasta su fi 40, abinda ya sanya al’umma ke tambayar ko tsarin tsaron Najeriya yana da nagarta.
AYPN ta zargi Ministan da fifita bukatun kansa na kasuwanci fiye da kare rayukan ‘yan kasa, inda suka kira shi da “dan kwangila da ke sanye da kayan soji.”
Sun kara da cewa ana raba kwangilolin tsaro ne bisa la’akari da goyon bayan siyasa, lamarin da ke hana isasshen kayan aiki da kuma samun bayanan sirri na tsaro.
AYPN ta yi ikirarin cewa Ministan ya fi mai da hankali kan muradun sa na siyasa, musamman takarar shugabancin kasa a 2027, maimakon sauke nauyin da ya rataya a wuyansa.
Matasa da ‘yan majalisa na matsa wa Shugaba Tinubu lamba ya sauke Ministan Tsaro Badaru kan tabarbarewar tsaro
