Idiat Adebule, mataimakiyar gwamnan jihar Lagos ta nesanta kanta daga takarar gwamnan jihar Akinwumi Ambode inda ta goyi babban abokin hamayyarsa Babajide Sanwo-Olu.
Ambode da Sanwo-Olu sune suke fafutukar ganin jam’iyar APC ta tsayar da daya daga cikinsu a zaɓen kujerar gwamnan jihar.
Da take magana a mazabarta bayan da ta kada kuri’arta a zaɓen fidda gwanin tarakar gwamnan ta sanar da goyon bayanta ga mutumin da jam’iyar take goyon baya a matsayin dantakara.
“Jam’iya ta zabi mutum wannan mutumin shine zan goyi bayansa kuma shi zanbi,”
Sanwo-Olu shine dantakarar da masu ruwa da tsaki na jam’iyar APC a jihar Lagos suke goyon baya.