
Hakkin mallakar hoto
Twitter/@BashirAhmaad
Manyan aminan siyasar tsohon gwamnan jihar Kano Rabi’u Musa Kwankwaso sun fice daga jam’iyyar PDP inda suka koma APC.
Wasu hotuna da mai taimaka wa shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, kan hanyoyin sadarwa na zamani, Bashir Ahmad, ya nuna aminan Kwankwaso irin su Farfesa Hafiz Abubakar da Aminu Dabo – tsohon shugaban hukumar kula ta tasoshin jiragen ruwan Najeriya – a fadar shugaban kasa ranar Alhamis da daddare.
“Shugaba Buhari ya yi maraba da wasu jagororin siyasar jihar Kano, cikin su har da Farfesa Hafiz Abubakar, tsohon mataimakin gwamna jihar wadanda suka komo jam’iyyarmu mai girma bayan sun fita daga wata jam’iyya,” in ji Bashir Ahmad.
Da ma dai tun a farkon mako ne ake rade-radin cewa ‘yan siyasar za su fita daga PDP su koma APC.
A watan Oktoba ne Farfesa Hafiz ya fita daga APC bayan ya gaza samun takarar gwamna a jam’iyyar.
Sai dai a wata wasika da ya aike wa shugaban jam’iyyar na mazabarsa ta Mandawari, Farfesa Abubakar, ya ce ya fita daga jam’iyyar ne domin radin kansa.
A watan Agusta ya sauka daga kujerar mataimakin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje sannan ya fice daga jam’iyyar APC ya koma PDP inda uban gidansa, Sanata Kwankwaso yake.
A wancan lokacin, Farfesa Hafiz Abubakar ya ce ya fita daga APC ne saboda gwamnan jihar yana barazana ga rayuwarsa.
Hakkin mallakar hoto
Twitter/@BashirAhmaad
Sai dai daga bisani ya koma PDP inda ya nemi tsayawa takarar gwamnan jihar a inuwar jam’iyyar.
Zabukan fitar da gwanin da aka yi a jam’iyyar reshen jihar Kano sun bar baya da kura sakamakon tsayar da Malam Abba Yusuf – surukin Sanata Kwankwaso – a matsayin mutumin da zai yi takarar gwamna a PDP.
Rahotanni sun ce wannan mataki bai yi wa wasu jiga-jigan jam’iyyar a jihar dadi ba, cikinsu har da Farfesa Abubakar, wanda ya yi tsammani shi za a tsayar a matsayin dan takara.