Manoman Kaduna Sun Koka Kan Tsadar Takin Zamani

Wasu manoma a jihar Kaduna sun bayyana damuwarsu kan yadda tsadar takin zamani ke barazana ga harkar noma a bana. Manoman sun ce hauhawar farashin takin na iya rage yawan amfanin gona da za a samu a bana.

Wani manomi, Malam Musa Ibrahim, ya shaida wa manema labarai cewa a bara ya sayi buhun takin NPK kan naira dubu goma sha biyar, amma yanzu ya haura naira dubu talatin. Ya ce hakan na hana manoma da dama samun isasshen taki don inganta noma.

Shi ma wani manomi daga yankin Zaria, Alhaji Shehu Abdullahi, ya ce gwamnati na bukatar daukar matakin rage tsadar takin domin kare fannin noma daga durkushewa.

A nasa bangaren, kwamishinan noma na jihar Kaduna ya tabbatar da kokarin gwamnati na shigo da taki domin saukaka wahalar da manoma ke fuskanta.

More from this stream

Recomended