Mambobin PDP da NNPP 216 Sun Sauya Sheƙa Zuwa Jam’iyyar APC a Jigawa

Akalla mambobi 216 na jam’iyyun PDP da NNPP sun sauya sheƙa zuwa jam’iyyar APC a karamar hukumar Gagarawa da ke jihar Jigawa.

An karɓi sabbin mambobin ne a hukumance yayin wani taron “Tattaunawar Jama’a da Gwamnati” da aka gudanar a shelkwatar karamar hukumar Gagarawa, wanda Gwamnan jihar, Malam Umar Namadi, da wasu manyan jami’an gwamnati suka halarta.

Gwamna Namadi ya bayyana cewa an shirya taron ne domin bai wa jama’a damar jin irin abubuwan da gwamnati ta cimma cikin shekaru biyu da suka gabata, da kuma gabatar da bukatu da ƙalubale da suke fuskanta.

Ya kara da cewa taron na bude ne ga kowane ɗan jihar Jigawa ba tare da la’akari da bambancin jam’iyya ba, tare da nanata shirinsa na ci gaba da sauraron koke-koke da kuma amsar su ta hanyar da ta dace.

Gwamna Namadi ya sake tabbatar da cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da aiwatar da ayyuka da shirye-shirye domin sauƙaƙa rayuwar jama’a da tabbatar da bunƙasar jihar Jigawa.

A yayin taron, wasu kwamishinoni shida daga ma’aikatu daban-daban sun gabatar da ayyukan da aka gudanar a yankin Gagarawa, ciki har da gina hanyoyi, shirye-shiryen tallafawa jama’a, gyaran asibitoci da makarantun gwamnati, da kuma asibitin Gagarawa da ke gab da kammaluwa.

Haka kuma an bayar da guraben aiki, tallafin karatu, da shirye-shiryen ƙarfafa mata a yankin.

More from this stream

Recomended