Majalisar Wakilai ta Najeriya ta gayyaci Daraktan Hukumar Sufurin Jiragen Kasa ta Kasa (NRC), Kayode Opeifa, da kuma Daraktan Kamfanin Railway Property Management Company Limited, Timothy Zalanga, domin bayyana a gaban kwamitinta kan harkokin sufuri na kasa da yadda ake tafiyar da kadarorin hukumar a fadin kasar.
Shugabar kwamitin majalisar kan harkokin sufuri na kasa, Hon. Blessing Onuh, ta bayyana cewa gayyatar ba wai don tsangwama aka yi ba, illa dai domin tabbatar da cewa hukumomin gwamnati suna aiwatar da aikinsu yadda ya kamata.
Wasu ‘yan kwamitin sun koka kan yadda ake tafiyar da kadarorin hukumar NRC da kuma zarge-zargen sayar da su ba bisa ka’ida ba, tare da korafin cewa wasu ma’aikata da ‘yan fansho na hukumar na fuskantar korafi daga gidajensu a yankunan ma’aikata.
Hon. Onuh ta jaddada cewa sashe na 88, 89, 128 da 129 na kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999 (wanda aka gyara) ya bai wa majalisa cikakken ikon sa ido kan ayyukan gwamnati, kuma kwamitinta ba zai zuba ido yana kallon abubuwa suna tafiya ba daidai ba.
Kwamitin ya umarci NRC da Railway Property Management Company Ltd su gabatar da muhimman takardu da suka shafi kasafin kudinsu na 2022, 2023 da 2024 da kuma kadarorinsu da yarjejeniyar hadin gwiwa da masu zaman kansu, kafin ranar Talata, 20 ga Mayu, 2025.
Ana sa ran Opeifa da Zalanga za su bayyana a gaban kwamitin a ranar Laraba, 21 ga Mayu, 2025.
Hon. Onuh ta ce kwamitin za ta yi aiki tare da masu ruwa da tsaki domin samun nasara a bangaren sufuri, musamman na jiragen kasa.
Majalisar Wakilai ta gayyaci Shugaban Hukumar Sufurin Jirgin Kasa da shugaban kamfanin Railway Property Management
