Majalisar dokokin jihar Kano ta kafa kwamitin bincike kan fefan bidiyon Ganduje

Majalisar dokokin jihar kano ta kafa wani kwamiti mai wakilai 7 da zai bincika sahihancin fefan bidiyon dake nuna gwamna, Abdullahi Umar Ganduje yana karbar kudi.

Jaridar Daily Nigerian da ake wallafawa a Intanet ce ta saki fefan bidiyon gwamnan wanda ake zargin yana karbar cin hanci daga yan kwangila.

An kafa kwamitin bayan da wakilin mazabar Warawa a majalisar,Labaran Abdul Madari ya gabatar da kudirin dake buƙatar kulawar gaggawa kuma ya samu goyon bayan, Dr Baffa Babba Danagundi.

Madari ya ce majalisar na da ikon bincike kan duk wani batu da zai shafi zaman lafiya a jihar.

Da yake magana ya yin zaman shugaban marasa rinjaye a majalisar,Baffa Babba Danagundi ya shawarci gwamnatin jihar da ta janye batun gurfanar da Jaridar gaban kotu kan fefan bidiyon.

A cewarsa kundin tsarin mulki ya bawa majalisar ikon binkicen lamari irin wannan.

Kwamitin zai samu shugabancin,Baffa Babba Danagundi.

Kwamitin zai kammala aikinsa cikin wata daya.

More News

Kwankwaso ya bada tallafin miliyan ₦50 ga mutanen da ambaliyar Borno ta shafa

Tsohon gwamnan jihar Kano kuma jagoran jam'iyar NNPP, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya bada tallafin naira miliyan 50 ga mutanen da ambaliyar ruwa a...

Sakamakon NECOn 2024 ya fito

Hukumar shirya jarabawar ta kasa ta fitar da sakamakon jarabawar kammala sakandare ta watan Yuni/Yuli 2024, inda kashi 60.55 cikin 100 na waÉ—anda suka...

Ƴan Najeriya na shan baƙar wahala—Janar Abdulsalami

Tsohon shugaban kasa, Janar Abdulsalami Abubakar, ya ce wahalhalun da ake fama da su a Najeriya na kara tabarbarewa, kuma rabon kayan agajin ba...

EFCC ta musalta cewa Yahaya Bello na tsare a ofishin hukumar

Hukumar EFCC dake yaƙi da masu yiwa tattalin arzikin ƙasa ta'annati ta ce tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello baya ya tsare a hannunta. A...