Mai Girma Gwamn Kano ya ɗauki nauyin jinyar Abdulrabba

Alhamdulillah, bayan sakonni da mutane ke ta turo mana daga ko’ina game da wannan bawan Allah ni da Baba Ali SSA HealthAffairs, mun sanar da mai girma Gwabnan Kano HE. Abba Kabir Yusuf halin da wannan bawan Allah ke ciki.

A kuma yau din Bava Ali ya tashi tashi takans ya je har garin su Abdurraba ya ga halin da su ke ciki, sannan ya sanar da su kulawarsa game da lafiyarsa gabadaya mai girma Gwabna ya dauki nauyi, duk da cewar aikin da zaa yi masa ba yanzu ba ne, asibitin Malam Aminu Kano yanzu sun dora shi akan shan magunguna na tsahon lokaci kafin ciwon ya dan sace sanna ayi aikin, Baba Ali ya tabbatar musu da duk abun da ya tashi koma menene da asibitin suka bukata su kira kaitsaye zaa yi musu, bisa umarnin mai Girma Gwabna.
Muna godiya ga mai girma Gwabna HE, bisa jin kukanmu da ya ke yi mu talakawan jihar Kano.

Daga Fauziyya D. Sulaiman
SSA Needy and Valnurble.

More from this stream

Recomended