Uwar Ahmed Musa, ɗalibin makarantar sakandaren fasaha da ke Kaduna wanda aka kashe bisa zalunci, ta bayyana a gaban kotu tana neman adalci, tana mai cewa “ba zan bar wannan lamarin haka ba.”
Rahotanni sun nuna cewa an tsinci gawar Ahmed Musa, ɗalibi mai shekaru 16 da ke aji biyar (SS2) a Government Technical College Malali, cikin ƙaramar hukumar Kaduna ta Arewa, a ranar 16 ga Fabrairu, 2025. An tsinci gawarsa a cikin harabar makarantar, hannu da ƙafafu daure.
Uwar marigayin, tare da ‘yan uwa da wasu da ke goyon bayanta, sun bayyana a kotun Majistare da ke Kabala Doki a Kaduna, inda ta nuna fushinta bisa yadda aka yi watsi da lamarin.
Ta kuma yi barazanar cewa za su fara zanga-zanga a faɗin jihar tare da kungiyoyin mata.
A halin da ake ciki, alkalin kotun Majistare, Naheed Ibrahim Abdulhamid, ya dage sauraron shari’ar har zuwa ranar 27 ga Mayu, 2025, bayan gaza samun halartar shaidu da suka haɗa da jami’an ’yan sanda da kuma waɗanda ake zargi da hannu a kisan.
Mahaifiyar Dalibin da Aka Kashe a Kaduna Ta Garzaya Kotu, Ta Bukaci a Yi Mata Adalci
