
Shugaban Hukumar Yaki Da Yiwa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati EFFC, Ibrahim Mustafa Magu yaki yarda ya amsa tambaya kan fefan videon gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje.
Akwai dai matsin lamba daga dai-daikun mutane dama kungiyoyin farar hula dake kiran hukumar ta EFCC kan ta binciki gwamnan.
Ya zuwa yanzu dai dukkannin hukumomin biyu dake yaki da ci hanci da rashawa wato ICPC da kuma EFCC ba su ce komai ba game da batun kisan.
Da yake amsa tambayoyin yan jaridu a hedkwatar hukumar ranar Litinin da fari dai Magu ya yi shiru kana ya yi dariya inda ya ce ” tambaya ta gaba.”
Amma kuma jaridar Daily Nigerian ta gano cewa a makon da ya wuce hukumar ta EFCC ta kaddamar da bincike cikin sirri kan fefan bidiyon na gwamna Ganduje.