Kungiyar Manyan Ma’aikata ta Kasa da Kamfanonin Gwamnati (SSASCGOC) reshen Kungiyar Kwadago ta Hukumar Kula da Abinci da Magunguna ta Kasa (NAFDAC) ta fara yajin aikin sai baba-ta-gani a kan rashin biyan buƙatun ma’aikata.
Mahimman batutuwan sun haɗa da sake duba sakamakon jarrabawar ƙarin girma na 2024, nada daraktoci don al’amuran jama’a/ayyuka na musamman da cibiyar horarwa, da sake fasalin yanayin jarrabawar ƙarin girma.
Ƙarin buƙatun sun haɗa da ƙirƙirar matsayin jami’in ilimin halayyar ɗan adam, biyan kuɗin jana’iza, siyan inshorar rai, biyan alawus na komawa gida, da biyan bashin albashi na 2022.
Sakataren kungiyar kwadago ta kasa (TUC), Ejor Michael, a cikin wata sanarwa da ya fitar, ya ce matakin yajin aikin ya biyo bayan cikar wa’adin kwanaki 14 da aka bayar a ranar 20 ga Satumba, 2024, bayan da mahukuntan hukumar suka kasa magance wadannan korafe-korafe.
Sanarwar ta kara da cewa, duk da taron da aka yi a ranar 4 ga watan Oktoba, inda aka ci gaba da tattaunawa, ba a cimma matsaya ba, wanda ya sa aka fara yajin aikin a fadin kasar daga ranar 7 ga watan Oktoban 2024.
Kungiyar ta umurci dukkan ma’aikatan da su dakatar da ayyukansu, da kwashe kayansu, tare da tabbatar da cewa babu wanda ya shiga ofisoshin hukumar ta NAFDAC yayin yajin aikin.