Lionel Messi ya yi nasara a Kotun Ƙoli kan amfani da sunansa a matsayin kamfani

lionel messi in friendly against Girona Sept 16 2020

Kotun Kolin Tarayyar Turai ta yanke hukuncin cewa dan wasan Barcelona Lionel Messi zai iya yin rijistar sunansa a matsayin kamfani bayan an kwashe shekara tara ana shari’a kan batun.

Kotun ta yi watsi da karar da kamfanin kekuna na Sufaniya mai suna Massi da kuma ofishin kula da hakkin mallaka na Tarayyar Turai suka daukaka a kan batun.

A shekarar 2011 ne dan wasan ya nemi a sanya sunansa a matsayin kamfani da tambari kan tufafi da sauran kayan wasanni.

Sai dai Massi ya ce tambarinsa da na Messi sun yi kama da juna kuma hakan zai iya haifar da rudani ga masu saye da sayarwa.

Kotun Kolin ta Turai ta ce za a iya yin la’akari da shaharar dan wasan idan ana son yanke hukunci kan ko jama’a za su iya bambancewa tsakaninsa da kamfanin kekuna idan sun je yin sayayya.

Daga nan ne kotun ta amince da hukuncin da wata kotun Turai ta yanke a 2018 cewa dan wasan ya yi shararar da za ta sa ba za a samu wani rudani ba wajen bambance kayan kamfaninsa da na Massi.

Tun da fari kamfani Massi, wanda ke sayar da tufafi da kayan tseren kekuna, ya yi nasara a karar da ya shigar kan da wasan na Barcelona. Sai dai ya sha kaye bayan da Lionel Messi ya daukaka kara zuwa wata kotun.

Messi, mai shekara 33, wanda ke sanya rigar wasa mai lamba 10, ya zama dan kwallon duniya sau shida kuma shi ne dan wasan da ya fi samun kudi, a cewar mujallar Forbes. Ta ce ya samu $126m (£97m) a shekarar 2020.

More News

Mai magana da yawun Tinubu ya ajiye aikinsa na wani lokaci

Mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai Ajuri Ngelale ya ajiye aikinsa na wani lokaci domin tunkarar matsalar lafiya.Mista Ngelale...

Ali Jita ya koma jam’iyar APC daga NNPP

Mataimakin shugaban majalisar dattawa dattawa, Sanata Barau Jibrin ya karɓi fitaccen mawakin Kannywood, Aliyu Isa Jita daga jam'iyar NNPP ya zuwa jam'iyar APC. Ali Jita...

An yi jana’izar mutumin da ya ƙirƙiri tutar Najeriya

Iyalan marigayi, Pa Taiwo Akinkumi mutumin da ya ƙirƙiro tutar Najeriya sun yi bikin binne shi bayan da gwamnatin tarayya ta gaza cika alƙawarin...

‘Za a ƙara wa ƴan bautar ƙasa na NYSC alawus’

Babban daraktan hukumar yi wa kasa hidima ta kasa (NYSC) Birgediya Janar Yushau Ahmed, ya tabbatar wa ‘yan bautar kasar cewa za a kara...