Likitoci sun ceci hannun wani mutum ta hanyar dasa shi a kafarsa

Likitoci a kasar China sun samu nasarar ceto hannun wani mutum ta hanyar dasa shi a ƙafarsa.

Hannun mutumin na hagu ya guntule ne bayan da ya gamu da hatsari a wurin aiki inda wata farfela mai kai fi ta yanke masa shi .Bayan da aka garzaya da shi asibiti likitoci sun yi kokarin yi masa tiyata domin ya cigaba da amfani da hannun da ya rasa kamar yadda yake a baya.

Tawagar likitoci masu tiyatar sun gaza hada hannun kai tsaye saboda jijiyoyin da kuma tsokar wurin na bukatar lokaci domin su warke sakamakon mummunan rauni da suka yi.

Hakan ne yasa suka dasa hannu a jikin naman kafarsa domin ya cigaba da samun jini har ya zuwa lokacin da za a hada shi da jikin ragowar hannun.

More from this stream

Recomended