Likita da aka yi garkuwa da shi ya sulale ya gudu daga hannun ƴan bindiga bayan an gama cinikin kuɗin fansa

Kungiyar likitocin Najeriya, NMA, ta tabbatar da kub’ɓucewar wani likitan da aka sace, Dokta Orockarrah Orock, da ke aiki a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Najeriya, UNTH, Ituku-Ozalla, Jihar Enugu.

An samu labarin cewa an yi garkuwa da Orock ma’aikacin Sashen Asthesia na UNTH a daren ranar Asabar a cikin harabar asibitin, yayin da yake bakin aiki.

Shugaban kungiyar NMA reshen jihar Enugu, Dr Celestine Ugwoke, shi ne ya tabbatar da hakan ga Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya a Enugu ranar Litinin.

Mista Ugwoke ya ce, Orock ya tsere ne bayan da masu garkuwa da shi suka gamsu da tayin biyan kudin fansa da matarsa ta nema kuma suka tafi suka yi barci mai nauyi.

A cewarsa, likitan da aka sace a hankali ya zarce daga inda aka ajiye shi a cikin kogon masu garkuwa da mutanen sannan ya samu ya gudu.

More News

Dakarun Najeriya sun cafke wasu ƴan’aiken ƴanbindiga a Kaduna

Sojoji sun kama wasu mutum biyu da ake zargi da kaiwa 'yan bindiga sakonninsu a kasuwar ƙauyen SCC da ke ƙaramar hukumar Kachia a...

Ƴansanda sun hallaka masu garkuwa da mutane

Ƴansanda sun hallaka wasu masu garkuwa da mutane uku da ake zargin sun yi yunkurin yin garkuwa da matar wani dan majalisar dokokin jihar...

Ƴanbanga sun sake kawar da wani ƙasurgumin ɗanbindiga

Rahotanni da ke fitowa daga Arewa maso Yammacin Najeriya na nuna cewa an yi nasarar kawar da wani fitaccen dan bindiga a jihar Zamfara,...

Ƴansanda a Katsina sun yi nasarar cafke wasu tantiran masu safarar alburusai wa ƴanbindiga

Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina a ranar Juma’a ta sanar da cewa ta kama wasu manyan ‘yan bindiga guda uku tare da kwato manyan...