Labarin ɓacewar al’aura ƙarya ne—Ƴan sanda

‘Yan sanda a Borno a ranar Talata sun yi watsi da rahoton bacewar al’aurar maza a Maiduguri.

Mai magana da yawun ‘yan sandan, ASP Nahum Daso, ya bayyana ikirarin da wasu suka yi a matsayin labari mara tushe.

Mista Daso ya bayyana cewa ‘yan sanda sun samu bayanan karya da wasu mutane ke yadawa kan bacewar al’aurarsu yawanci bayan sun yi musabaha da baƙi.

Ya kara da cewa wadanda abin ya shafa da suka kai kara an kai su asibiti domin duba lafiyarsu sai dai an gano cewa zargin ba shi da tushe balle makama domin al’aurarsu na nan daram kuma tana aiki.

“Akan haka ‘yan sanda na son sanar da mutanen Borno kada su firgita; su kasance masu bin doka da oda tare da yin watsi da bayanan da ba su dace ba da ke iya haifar da rashin jituwa da rushe yanayin zaman lafiya a jihar.

More News

Ƴansanda sun hallaka masu garkuwa da mutane

Ƴansanda sun hallaka wasu masu garkuwa da mutane uku da ake zargin sun yi yunkurin yin garkuwa da matar wani dan majalisar dokokin jihar...

Ƴansanda a Katsina sun yi nasarar cafke wasu tantiran masu safarar alburusai wa ƴanbindiga

Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina a ranar Juma’a ta sanar da cewa ta kama wasu manyan ‘yan bindiga guda uku tare da kwato manyan...

Tinubu ya amince da mafi karancin albashi na N70,000

Shugaba Bola Tinubu ya amince da N70,000 a matsayin mafi karancin albashi ga ma’aikatan Najeriya, inda ya yi alkawarin sake duba dokar mafi karancin...

Mutanen Isra’ila sama da rabin miliyan sun tsere saboda yakin Gaza

Mutanen Isra'ila sama da rabin miliyan ɗaya ne suka fice daga ƙasar kuma ba su koma ba a watanni shida na farkon yaƙin Isra'ila...