Kungiyar Kwadago ta Najeriya ta nemi Shugaba Bola Tinubu da ya janye ƙarin farashin man fetur

Daga Sabiu Abdullahi

Kungiyar Kwadago ta Najeriya (NLC) ta soki gwamnatin Shugaba Bola Tinubu kan karin farashin man fetur da aka yi ranar Laraba tana mai cewa hakan yunkuri ne na kara lalata tattalin arzikin kasar da jefa jama’a cikin talauci da rashin aikin yi.

A wata sanarwa mai taken “Me Ke Tafe Bayan Karin Farashin Man Fetur?” wacce Shugaban NLC na kasa, Kwamared Joe Ajaero ya sanya wa hannu, kungiyar ta nuna damuwa kan ci gaba da karuwar farashin mai ba tare da an yi wani tanadi na rage radadin hakan ba.

Sanarwar NLC ta bayyana cewa, “Mun yi matukar damuwa da karin farashin man fetur da aka yi. A fili yake cewa abin da kawai wannan gwamnati ta sani shi ne kara farashin man fetur ba tare da la’akari da halin da al’ummar Najeriya ke ciki ko kuma daukar matakan rage wa jama’a radadi ba.”

Sabon karin da ya kai farashin man fetur N1030 a kowanne lita ya zo ne bayan karin da aka yi watanni kadan da suka gabata inda farashin ya haura zuwa fiye da N850 a kowacce lita.

NLC ta kalubalanci gwamnatin da ta fitar da wasu ingantattun manufofin bunkasa tattalin arziki da cigaban kasa maimakon daukar matakai na wucin gadi ba tare da tsarin da zai dore ba da kuma sanya tsarukan tallafi.

Kwamared Ajaero ya bayyana cewa karin zai kara jefa talakawa cikin matsin rayuwa, rage karfin masana’antu, tare da haifar da rasa ayyukan yi.

An ruwaito shi yana cewa, “Saboda haka, muna kira ga gwamnati da ta gaggauta janye wannan karin farashi kamar yadda karin da aka yi a baya bai kawo wani ci gaba ba. Maimakon haka, mutane sun dada talaucewa.”

Kungiyar NLC ta kuma yi kira ga gwamnatin Shugaba Tinubu da ta fito fili ta bayyana manufofinta game da makomar kasar.

Shugaba Bola Tinubu, wanda ya karbi ragamar mulki a watan Mayun 2023, ya sha suka kan tsauraran manufofin tattalin arzikinsa.

More News

Sojoji sun lalata haramtattun matatun mai 32 a yankin Neja Delta

Dakarun sojan Najeriya na runduna ta 6 dake Fatakwal sun samu nasarar lalata haramtattun matatun man fetur 32 tare da ƙwace lita 250,000 na...

An gudanar da bikin cikar Kwankwaso shekara 68.

Tarin magoya baya da kuma abokanan siyasar tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabi'u Kwankwaso ne suka halarci taron lakca da aka shirya domin bikin...

Faruk Lawan ya kammala zaman gidan yarin Kuje

An sako tsohon ɗan majalisar wakilai ta tarayya, Hon Faruk Lawan daga gidan yarin Kuje bayan da ya kammala zaman gidan yarin na shekaru...

Sojojin Najeriya Sun Musanta Jita-jitar Mutuwar Babban Hafsan Sojojin Ƙasa, Laftanar Janar Taoreed Lagbaja

Daga Sabiu AbdullahiRundunar Sojojin Najeriya ta karyata rahotannin da ke yawo a kafafen sada zumunta cewa Babban Hafsan Sojojin Ƙasa, Laftanar Janar Taoreed Lagbaja,...