Kun san tanadin doka kan rikicin ‘yar takarar APC a Zamfara?

Gwamnan jihar Zamfara Abdul'aziz Yari Abubakar


Gwamnan Zamfara ya yi ikirarin gudanar da zaben fitar da ‘yan takara

Masana shari’a sun bayyana matsayin doka game da batun matsayin fitar da ‘yan takarar jam’iyyar APC a jihar Zamfara.

Masanan sun ce cikar wa’adin lokacin gudanar da zaben fitar da ‘yan takara na hukumar zabe ba zai zama dalilin hana wa jam’iyya gabatar da sunayen ‘yan takararta ba.

Barrister Abdulhamid Muhammed ya shaidawa BBC cewa lokacin gudanar da zaben fitar da ‘yan takara na hukumar zabe ba zai zama doka ba, illa abin da dokar zabe ta tanada.

“Kundin dokar zabe na kasa, sashe na 31 ya nuna jam’iyyu suna da kwanaki 60 kafin zabe domin gabatar da ‘yan takara,” in ji shi.

Ya ce ba za a yi laka’ari da jadawalin da hukumar zabe ta tsara ba domin fitar da ‘yan takara, illa tanadin da dokar zabe ta yi.

“Sai Idan an saba wa kwanaki 60 kafin zabe za a iya cewa jam’iyya ta rasa dan takara kuma dole ta rungumi kaddara.”

Hakan dai na nufin Jam’iyyar APC na da damar gabatar da ‘yan takararta na gwamna da na ‘yan majalisa a jihar Zamfara duk da zaben fitar gwani na jam’iyyar ya gagara.

Barista Abdulhamid ya ce kundin zaben ya nuna cewa hukumar zabe ba ta da ‘yancin kin amincewa da ‘yan takarar da aka mika ma ta kafin cikar wa’adin doka na mika sunayen ‘yan takara.

“Keta wa’adin Jadawalin hukumar zabe na fitar da ‘ya takara ba ya cikin tsarin doka.” In ji shi.

Ya kara da cewa hukumar zabe takan tsara jadawalinta na harakokin da suka shafi zaben fitar da ‘yan takara saboda tanadin muhimman ayyukan da ke gabanta na zabe.

Jam’iyyar APC dai ana ganin za ta iya rasa damar gabatar da ‘yan takara bayan ta kasa gudanar da zaben fitar gwani na ‘yan takarar saboda rikicin siyasa tsakanin bangarorin jam’iyyar a jihar

.

More from this stream

Recomended