Wata kotun majistare da ke zaune a Akure, babban birnin jihar Ondo, ta ba da umarnin a tsare wani mutum mai suna Moses Udoh a gidan yari bisa zargin cin zarafin ‘yarsa mai shekaru 11.
An cafke wanda ake zargin ne ta hannun jami’an rundunar ‘yan sandan jihar bisa zargin aikata laifin a unguwar Igboniki, Akure, makon da ya gabata.
An gurfanar da Udoh a gaban kotu kan tuhumar da suka hada da cin zarafin karamar yarinya da kuma barazanar kashe rai.
A lokacin zaman kotun a ranar Alhamis, mai gabatar da kara, Insifekta Taiwo Oniyere, ya shaida wa kotu cewa wanda ake zargi ya sha yin jima’i da karfin tsiya da ‘yarsa mai shekaru 11, wanda hakan ya janyo mata rauni.
Haka kuma, Oniyere ya bayyana cewa wanda ake zargin ya yi barazanar kashe yarinyar idan ta kuskura ta gayawa wani game da abin da ya aikata.
A cewar mai gabatar da kara, laifukan da ake tuhumar wanda ake zargin sun saba wa Sashe na 25(a) da 86(2) na dokar hana cin zarafi da ke jihar Ondo ta shekarar 2021.
Kotun Majistare ta umarci a tsare wani mutumi a gidan yari kan zargin lalata da ƴarsa mai shekaru 11
![images-2024-12-06T045605.542.jpeg](https://arewa.ng/wp-content/uploads/2024/12/images-2024-12-06T045605.542.jpeg)