Kotun Daukaka Kara ta sauraron karar zaben kananan hukumomi a Jihar Benue, wadda ke zama a gidan NBA da ke Abuja, na shirin yanke hukunci kan wasu korafe-korafe da suka taso daga zaben kananan hukumomi da aka gudanar a ranar 5 ga Oktoba, 2024.
Kananan hukumomin da abin ya shafa sun hada da Gboko, Tarka, Makurdi, Gwer West, Gwer East, Guma da Buruku.
Wannan hukunci na daga cikin mafiya jiran sakamako, duba da yadda aka shafe makonni ana tattaunawa da kwararrun lauyoyi da kuma irin bincike mai zurfi da aka gudanar kan yadda aka gudanar da zaben da kuma sakamakon da aka fitar.
A baya dai, an kafa wannan kotu ta musamman domin duba daukaka karar da ta fito daga hukuncin kotun sauraron kararrakin zaben kananan hukumomi ta farko.
Kotun, karkashin jagorancin Mai Shari’a Dennis Igyuse, tare da wasu mambobi biyu – Mai Shari’a Michael Ugar da Mai Shari’a Maimuna Ikwulono – ta fara zaman nata ne a Makurdi, amma daga bisani aka mayar da ita Abuja a watan Maris na 2025 saboda dalilan tsaro da kuma yajin aikin ma’aikatan shari’a.
Kotun Daukaka Karar Zaben Kananan Hukumomi a Benue Za Ta Yanke Hukunci A Yau
