Wata kotu a ƙasar Birtaniya ta yanke wa Adewale Kudabo, tsohon ma’aikacin asibitin York, hukuncin ɗaurin shekara guda a gidan yari bisa samunsa da laifin cin zarafin wata mara lafiya.
Alkalin kotun, Alex Menary, ya bayyana cewa Kudabo “ya ci amanar aikin jinya” da aka ɗora masa.
Kudabo ya amsa laifin aikata laifuffuka biyu na cin zarafin jiki tun ranar farko da shari’arsa ta fara a watan Afrilu. Kotun ta yanke masa hukunci a ranar 10 ga Yuni, inda aka ce zai yi rabin shekara kafin a iya sakin sa.
Lauyan gwamnati, Henry Fernnandez, ya shaida wa kotu cewa Kudabo ya yi wa marar lafiyar wanka, sannan ya sumbace ta a leɓe duk da tana cikin raɗaɗi. Bayan ‘yan kwanaki, ya sake tambayar ta ko tana son wani wankan, sannan ya ƙara yunkurin sumbatar ta.
Asibitin York da hukumar NHS da ke kula da shi sun nemi afuwa daga marar lafiyar. Hukumar ta ce Kudabo ya bar aikin sa jim kaɗan bayan faruwar lamarin.
Lauyan Kudabo, Jerry Sodipe, ya ce bai taɓa samun laifi ba a baya kuma ya nuna nadama. “Ya amince da laifinsa – bai kamata ya aikata hakan ba,” in ji Sodipe.
An bayyana cewa Kudabo ya zo Birtaniya ne daga Najeriya tare da iyalinsa domin neman aiki, amma yanzu ya rasa aikinsa bayan faruwar lamarin.
Kotun Birtaniya Ta Yanke Wa Ɗan Najeriya Hukuncin Dauri Saboda Sumbatar Mara Lafiya
