Kotu ta tsare matashi kan zargin lalata da yarinya ƴar shekara 13

Kotun majistare ta Badagry da ke Legas a ranar Alhamis, ta bayar da umarnin tsare wani matashi dan shekara 28, Stanley Amos, da ake zargi da lalata wata yarinya ‘yar shekara 13.

Alkalin kotun, Patrick Adekomaiya, ya bayar da umarnin a tsare Amos a gidan gyaran hali na Awarjigoh da ke Badagry bayan ya ki amsa laifinsa.

Alkalin kotun ya kuma bayar da umarnin cewa a kwafi fayil din karar sannan a aika zuwa ofishin daraktan kararrakin jama’a domin samun shawarwarin shari’a.

Tun da farko, dan sanda mai shigar da kara, Ayodele Adeosun, ya shaida wa kotun cewa wanda ake tuhuma ya aikata laifin ne a ranar 22 ga watan Satumba, 2024.

Adeosun ya ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 3:00 na rana a unguwar Caroline da ke Aradagun, Badagry, jihar Legas.

A cewar mai gabatar da karar, laifin ya ci karo da sashe na 137 da 261 na dokar laifuka ta jihar Legas a shekarar 2015.

Sakamakon haka, Alkalin Kotun, Adekomaiya, ya dage ci gaba da sauraron karar har zuwa ranar 25 ga watan Nuwamba, 2024, domin yanke hukunci kan neman belin Amos da kuma shawarar lauyan DPP.

More News

Wasu matasa uku da ake zargi da garkuwa da mutum sun gurfana a gaban kotu a Kano

Wasu matasa guda uku sun bayyana a gaban wata kotun majistire dake zamanta a unguwar Gyadi-Gyadi dake Kano inda ake tuhumarsu da zargin  yin...

EFCC ta kama tsohon gwamnan Taraba Darius Ishaku

Hukumar EFCC dake yaƙi da masu yiwa tattalin arzikin ƙasa zagon ƙasa ta kama Darius Ishaku tsohon gwamnan jihar Taraba kan zargin al-mundahanar kuɗaɗen...

Kotu ta ɗaure waɗanda suka yi fashi a bankin Offa da ke jihar Kwara a 2018

Mai shari’a Haleemah Salman ta babbar kotun jihar Kwara da ke zamanta a Ilorin a jiya ta yanke hukuncin kisa ta hanyar rataya ga...

Gwamnatin Najeriya ta kara wa ƴan bautar ƙasa na NYSC ‘alawee’ zuwa N77,000

Gwamnatin tarayya ta kara yawan alawus din masu yi wa kasa hidima (NYSC) zuwa N77,000 duk wata, daga Yuli 2024.  Wannan ci gaban ya...