Wata babbar kotun tarayya da ke Legas ta yanke hukunci na ƙarshe kan kuɗaɗe da kadarori da ake alaƙantawa da tsohon gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele, inda ta mallaka su ga hukumar yaƙi da rashawa, EFCC.
Mai shari’a Yellim Bogoro ce ta yanke wannan hukunci bayan EFCC ta shigar da ƙara tana neman a mallaka wa gwamnatin tarayya wadannan kadarori.
A cewar lauyar EFCC, Bilkisu Buhari-Bala, kuɗaɗen da aka ƙwace sun haɗa da dala miliyan 4.7 da naira miliyan 830, waɗanda aka ajiye a asusun bankuna daban-daban, ciki har da First Bank, Titan Bank, da Zenith Bank. Wadannan asusun dai na ƙarƙashin wasu mutane da kamfanoni kamar su Omoile Anita Joy, Deep Blue Energy Service Limited, Exactquote Bureau De Change Ltd, Lipam Investment Services Limited, Tatler Services Limited, Rosajul Global Resources Ltd, da TIL Communication Nigeria Ltd.
Kotu ta kuma ƙwace wasu kadarori da dama da ke Legas, waɗanda za a miƙa ga EFCC don mallaka wa gwamnatin tarayya.
Kotu Ta Mallaka Wa EFCC Kuɗaɗe da Kadarorin Tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeriya
