Wata babbar kotun tarayya da ke Kano ta yanke hukuncin mayar da Ado Bayero a matsayin Sarkin Kano.
Kotun ta yi watsi da dokar masarautar Kano ta 2024, wadda ta rusa masarautun jihar Kano guda biyar, har ta kai ga tsige Bayero daga karagar mulki.
Mai shari’a Abdullahi Muhammad Liman ne ya yanke hukuncin a ranar Alhamis, inda ya umurci dukkan bangarorin da su ci gaba da kasancewa a halin da ake ciki.
Wannan lamari dai ya soke matakin da gwamnatin jihar Kano ta dauka na soke dokar da ta kafa masarautu tare da nada Bayero a matsayin Sarkin Kano na 15.