Kamfanin mai na Nigerian National Petroleum Company Limited ya shirya daukar karin ma’aikata.
Kakakin kamfanin na NNPC, Olufemi Soneye, ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a.
Soneye ya ce za a dauki ma’aikata ne na mukamai daban-daban a sassa daban-daban na kamfanin makamashi.
Ya umurci masu bukata da su ziyarci shafin ma’aikata na NNPC don cike fom din neman aikin
“NNPC Ltd na farin cikin sanar da cewa a halin yanzu muna daukar ma’aikata da yawa a sassa daban-daban. Muna neman mutane masu hazaka da sadaukarwa don shiga kamfaninmu. Ziyarci shafinmu na sana’o’i don neman umarnin cike aikace-aikacen,” in ji Soneye.
A cikin wani sabon bayanin da ya sake, Soeye ya bayyana cewa saboda yawan zirga-zirgar da ba a taba gani ba a shafin yanar gizon NNPC Ltd daga masu neman guraben aiki, a halin yanzu shafin yana fuskantar tafiyar hawainiya.
“Masana na’urorinmu suna aiki tukuru don gyara matsalar.