Jirgin Yakin Amurka Ya Faɗa Cikin Teku

Wani jirgin yakin Amurka kirar F-18 ya fada cikin Tekun Red Sea a ranar Talata, bayan kasa tsayawa yadda ya kamata a saman dandalin saukar jirage na jirgin ruwan rundunar sojin ruwa, Harry S. Truman.

Rahotannin daga kamfanin labarai na Reuters sun bayyana cewa jami’an gwamnatin Amurka biyu ne suka tabbatar da faruwar lamarin, sai dai sun nemi a sakaya sunayensu.

Daya daga cikin jami’an ya bayyana cewa jirgin ya kasa yin sauka cikin nasara, lamarin da ya sa ya zame daga saman jirgin ruwan zuwa cikin teku.

A cewarsa: “Dukkan matukan jirgin biyu sun yi amfani da kujerun katsewa (ejection seats) kafin jirgin ya fada ruwa, kuma an ceto su ta hanyar jirgin daukar gaggawa.”

Wani jami’in na daban ya bayyana cewa matukan sun samu raunuka kadan, sannan babu wani daga cikin ma’aikatan dandalin jirgin da ya jikkata. Har zuwa lokacin wallafa wannan rahoto, rundunar sojin ruwan Amurka ba ta fitar da wata sanarwa ba a hukumance.

More from this stream

Recomended