Jirgi ya fadi a teku dauke da fasinjoji sama da 180

A shekara ta 2013 jirgin na Lion Air ya fada a teku sai dai dukkanin fasinjojinsa sun tsira da rayukansu

A shekara ta 2013 jirgin na Lion Air ya fada a teku sai dai dukkanin fasinjojinsa sun tsira da rayukansu

Wani jirgin saman fasinjar Lion Air ya yi hadari a teku Java jim kadan bayan tashinsa daga birnin Jakarta na Indonesia.

Fasinjoji fiye da 180 ke cikin jirgin Kirar Boeing 737, wanda ke kan hanyar zuwa yankin Pangkal Pinang da ke tsibirin Bangka.

Tuni aka tura tawagar masu bincike da aikin ceto yankin, sai dai babu tabbacin ko an samu wadanda suka rage da sauran rai.

Jami’ai da ke aiki a kamfanin man kasar ta Indonesia sun ce sun ga tarkacan jirgin, ciki harda kujerun fasinjoji a cikin ruwa da ke kusa da inda suke aiki a teku.

Shugaban kamfanin jirgin ya bayyana cewa a yanzu ba za su iya cewa komai ba a game da hadarin, inda ya ce suna kokarin tattara bayanai ne.

Jirgin dai yara aiki ne a 2016, sannan kuma ya zamo mallakin Lion Air ne a watan Augustan da ya wuce.

Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

‘Yan uwan fasinjojin jirgin sun shiga alhini a Jakarta

  • Kun san sojan da ya rasu a hatsarin jirgi a Abuja?
  • Mutum 257 sun mutu a hatsarin jirgi a Aljeriya

Wani jami’i a hukumar sufuri ta kasar ya shaidawa BBC cewa dama jirgin yana da ‘yan matsalolinsa tun da aka kawo shi kamfanin.

Yawanci al’ummar kasar ta Indonesia sun raja’a ne a kan tafiye-tafiye a jirgin sama, amma kuma mafi akasarin jiragensu na da ‘yan matsaloli nan da can.

Indonesia na cikin kasashen da ke fuskantar koma baya a harkokin sufurin jiragen sama, ko a shekarun baya-baya nan ta fuskanci irin wadanan hadura.

More News

Kwankwaso ya bada tallafin miliyan ₦50 ga mutanen da ambaliyar Borno ta shafa

Tsohon gwamnan jihar Kano kuma jagoran jam'iyar NNPP, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya bada tallafin naira miliyan 50 ga mutanen da ambaliyar ruwa a...

Sakamakon NECOn 2024 ya fito

Hukumar shirya jarabawar ta kasa ta fitar da sakamakon jarabawar kammala sakandare ta watan Yuni/Yuli 2024, inda kashi 60.55 cikin 100 na waÉ—anda suka...

Ƴan Najeriya na shan baƙar wahala—Janar Abdulsalami

Tsohon shugaban kasa, Janar Abdulsalami Abubakar, ya ce wahalhalun da ake fama da su a Najeriya na kara tabarbarewa, kuma rabon kayan agajin ba...

EFCC ta musalta cewa Yahaya Bello na tsare a ofishin hukumar

Hukumar EFCC dake yaƙi da masu yiwa tattalin arzikin ƙasa ta'annati ta ce tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello baya ya tsare a hannunta. A...