Jihohin biyu ne kadai za su iya mafi karancin albashi na ₦30000

Ƙungiyar Gwamnonin Najeriya, ta ce bayan jihar Lagos da Rivers babu wata jiha a Najeriya da zata iya biyan ₦30,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi.

Shugabannin kungiyar kwadago da kuma wakilan gwamnati sune suka cimma dai-daito kan mafi karancin albashin dai-dai lokacin da yan kungiyar kwadagon suke shirin tsunduma yajin aiki.

An gabatarwa shugaban kasa Muhammad Buhari rahoto kan mafi karancin albashin inda ya yi alkawarin duba rahoton kana ya sanar da jama’a matsayar da gwamnati za ta dauka.

Amma a wani taron gaggawa da suka gudanar ranar Laraba kan mafi karancin albashin, gwamnonin sun ce biyan ₦30,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi zai sa jihohin su talauce.

Saboda haka suka yanke shawarar kafa wani sabon kwamiti da zai gana da shugaban kasa Buhari kan batun.

More from this stream

Recomended