Jihar Borno ta kara kudin masaukin Alhazai na 2024

Gwamna Babagana Zulum na jihar Borno ya bayyana karin kudin masaukin maniyyata aikin hajjin 2024.

An kara kudin ne zuwa Riyal ma Saudiyya 3,450 ga kowane mahajjaci, karin Riyal 450 daga Riyal 3,000 na farko.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a yayin kaddamar da kwamitin Amirul Hajj mai mutane 23, karkashin jagorancin Sen. Kaka Shehu-Lawan, tare da Mohammed Dawule-Mainok a matsayin sakatare.

Kwamitin dai yana da alhakin tabbatar da gudanar da aikin Hajji cikin sauki.

A cewar Gwamna Zulum, “ana bukatar maniyyata su san lambobin dakinsu kafin su isa wurin, sannan a bar masu son zama tare su yi hakan.“

Ya kuma bayyana cewa, wajibi ne alhazai su kiyaye ka’idojin da aka tsara, domin duk wanda ya rasa jirgi zai jira jirgi na karshe idan akwai sarari.

More from this stream

Recomended