Jam’iyar NNPP ta lashe zaɓen ƙananan hukumomin jihar Kano

Jam’iyar New Nigeria People Party NNPP ta lashe zaɓen  dukkanin kujerun ƙananan hukumomin jihar Kano 44.

Farfesa Sani Malumfashi shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar Kano KANSIEC shi ne ya sanar da sakamakon a babban birnin jihar.

Ya ce an gudanar da zaben cikin tsari kuma lami lafiya ba tare da rahoton samun rikici ba a ko’ina.

Zaɓen kafin a gudanar da shi an yi ta samun takun saka tsakanin jam’iyar APC da kuma hukumar zaɓen bayan da wani mamba a jam’iyar APC ya kai hukumar zaɓen jihar ƙara a gaban kotu.

A ranar 22 ne ga watan Oktoba babban kotun tarayya dake Kano ta yanke hukuncin cewa Malumfashi bai cancanci shugabancin hukumar zaɓen ba.

Alƙalin kotun mai shari’a, Simon Amobede  da yake yanke hukuncin ya ce Malumfashi halastaccen ɗan jam’iyar NNPP kuma hakan ya saɓawa doka.

Sai dai a ranar Juma’a babbar kotun jihar Kano ta bawa hukumar zaɓe ta KANSIEC damar gudanar da zaɓen ƙarƙashin shugabancin Malumfashi.

More News

Jihar Neja za ta riƙa biyan  ₦80,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi

Gwamnan jihar Neja, Umar Bago ya amince a riƙa biyan ₦80,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi ga ma'aikatan jihar. Gwamnan ya amince da fara biyan...

Jam’iyar NNPP ta lashe zaɓen ƙananan hukumomin jihar Kano

Jam'iyar New Nigeria People Party NNPP ta lashe zaɓen  dukkanin kujerun ƙananan hukumomin jihar Kano 44. Farfesa Sani Malumfashi shugaban hukumar zabe mai zaman kanta...

Wani sojan ruwan Najeriya ya hallaka abokin aikinsa a Zamfara

Hedikwatar Tsaron Najeriya ta kama wani sojan ruwa mai suna A. Akila bisa zarginsa da kashe abokin aikinsa.An tura Akila zuwa sansanin Forward Operating...

Tinubu da Atiku sun haɗu a Masallacin Abuja

Shugaban ƙasa, Bola Ahmad Tinubu  sun haɗu da tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar a babban masallacin ƙasa dake Abuja. Mutanen biyu sun haɗu ne...