Jam’iyar APC ta kafa kwamitin sulhu

Kwamitin zartarwar jam’iyar APC na kasa ya kafa kwamiti shida da aka dorawa nauyin sasanta rikicin da ya biyo bayan zabukan fidda gwani da jam’iyar ta gudanar.

Zabukan fidda gwani da jam’iyar ta gudanar sun bar baya da kura a jihohi daban-daban dake fadin tarayyar ƙasarnan.

Ya zuwa yanzu dai hukumar zabe ta INEC ta ki yarda jam’iyar APC ta tsayar da yan takara a jihar Zamfara bayan da jam’iyar ta gaza gudanar da zaben cikin lokacin da dokar zabe ta tanada.

Gwamna, Rochas Okorocha na jihar Imo da takwaransa na jihar Ogun, Ibikunle Amosun dama na jihar Zamfara Abdulaziz Yari dukkanninsu suna cikin fushi bayan da yan takarar da suke goyon baya suka gaza cimma gaci a zaben fidda gwanin yan takarar gwamna a jihohin su.

Dukkannin gwamnonin jam’iyar 19 mambobi ne a kwamitin sasantawar dake kunshe da wasu fitattun yan jam’iyar.

Ga jerin sunayen yan kwamitin da kuma shiyar da za su gudanar da aikinsu:

Yankin Kudu maso gabas

1. Abdullahi Ganduje (shugaba)

2. Samuel Lalong

3. Kayode Fayemi

4. Godswill Akpabio

5. Umaru Dembo

6. Nasiru Aliko Koki

7. Ify Ugo Okoye

Arewa ta tsakiya

1. Ibrahim Geidam (shugaba)

2. Godwin Obaseki

3. Rotimi Akeredolu

4. Jibrilla Bindow

5. Pius Akinyelure

6. Vivian Chukwuani

7. Audu Ogbe

Kudu maso yamma

1. Kashim Shettima (shugaba)

2. Nasir el-Rufai

3. Akinwumi Ambode

4. Modupe Adelabu

5. Dakuku Peterside

6. Ken Nnamani

7. Seida Bugaje

Arewa maso yamma

1. Abiola Ajimobi (shugaba)

2. Mohammed Abdullahi Abubakar

3. Yahaya Bello

4. Adamu Aliero

5. Danjuma Goje

6. Jim Nwobodo

7. Fati Balla

Kudu maso kudu

1. Rauf Aregbesola (shugaba)

2. Atiku Bagudu

3. Abubakar Sani Bello

4. Gbemisola Saraki

5. Emeka Wogu

6. Sullivan Chime

7. Aleluchi Cookey-Gam

Arewa maso gabas

1. Umaru Tanko Al-Makura (shugaba)

2. Aminu Masari

3. Abubakar Badaru

4. Jumoke Anifowoshe

5. Matthew Omegara

6. Hafsat Mohammed Baba

7. Abdullahi Aboki

More from this stream

Recomended