Jami’an Tsaro a Amurka Sun Bazama Neman Ƙaramin Jirgi da Ya ɓace a Alaska

Jami’an tsaro a Amurka sun bazama domin neman wani ƙaramin jirgin sama mai ɗauke da mutum 10 da ya ɓace a jihar Alaska.

Masu kula da harkokin teku a yankin sun bayyana cewa jirgin, samfurin Cessna Caravan, ya ɓace ne a daidai lokacin da yake tafiya daga Unalakleet zuwa Nome, wata tazara mai nisan kilomita 19.

A cikin wata sanarwa da hukumomin jihar suka fitar, an bayyana cewa jami’an ceto na ci gaba da ƙoƙarin gano inda jirgin yake.

Rahotanni daga sashen kula da al’umma na Alaska sun tabbatar da cewa jirgin yana ɗauke da mutum 10—fasinjoji 9 da matuƙi guda ɗaya. Sai dai har yanzu ba a samu cikakken bayani kan halin da mutanen ke ciki ba.

Jihar Alaska na daga cikin yankunan da ke da tsaunuka da kuma yanayi mai tsauri, wanda ke haddasa haɗurran jirgin sama fiye da sauran jihohin Amurka.

More from this stream

Recomended