
Hukumar Kwastam ta Najeriya ta kama buhunan shinkafa mai nauyin 50kg guda 8413 da kuma galan din mai mai nauyin lita 25 guda 524, a wani kauye dake jihar Kwara.
Shugaban tawagar jami’an da suka samu nasarar kwato kayayyakin, DC.Abdullahi Musa Kirawa ya ce rundunar a shirye take ta kawo karshen illar fasa kaurin kayayyaki.
Da yake magana ya yin wani taron manema labarai domin nuna kayayyakin da suka kwace cikin kwanaki huɗu a aikin da suke a shiyar, Kirawa ya ce abubuwan da suka jawo jawabin ga yan jaridun sun faru ne cikin kwanaki huɗu.
Ya ce an gano kayayyakin a kauyen Onikan dake karamar hukumar Moro ta jihar.
Ya kara da cewa dukkanin gidajen kauyen an mayar da su kananan dakunan ajiye kayayyaki inda ake boye kayan da akayi fasa kauri.
A karshe ya yi kira ga masu riƙe da sarautar gargajiya dake yankin kan su fadakar da mutanensu illolin dake tattare da fasa kauri ga cigaban tattalin arzikin kasa.