Jami’an DSS sun bincike jirgin Atiku bayan da ya dawo daga Dubai

Jami’an hukumar tsaro ta DSS sun bincike jirgin tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar.

Jirgin mallakin dan takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyar PDP ya sauke shi ne a filin jirgin saman Abuja bayan da ya dauko shi daga birnin Dubai.

Paul Ibe, mai magana da yawun Atiku ya tabbatarwa da jaridar The Cable faruwar lamarin.

Jirgin dake dauke da Atiku daga Dubai ya sauka a filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe dake Abuja da misalin 1:30 na rana inda jami’an tsaro suke dakon saukarsa.

Wasu majiyoyi dake da masaniya kan abin da ya faru sun ce jami’an na DSS,dana hukumar shige da fice da kuma na hukumar Kwastam sun binciki Atiku da kuma jirgin saman.

A wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter Atiku ya ce an yi haka ne domin a tsorata shi kuma hakan ba zai sa ya tsorata ba.

More from this stream

Recomended