Jami’an hukumar hana fasa kwauri ta kasa wato Custom sun harbe wani direban mota da ake zargi da yin fasa kwaurin shinkafa a jihar Katsina.
Wani sheda ya bayyana cewa lamarin ya faru ne a jiya ranar Lahadi akan hanyar Dutsinma, wajen kwalejin ilimi ta tarayya.
Ya ce marigayin wanda yake tuka mota kirar J5 ya yi kokarin gujewa kamun jami’an na Custom lokacin da ya hangesu inda su kuma suka bude masa wuta.
Ƴansanda sun dauke gawar mamacin wanda har yanzu ba a gane inda ya fito ba.
Mai magana da yawun rundunar ƴansanda jihar Katsina, DSP Gambo Isa ya ce an ɗauki mutumin da ake zargi ya zuwa asibiti inda aka tabbatar da mutuwarsa.
Ya ce rundunar ta kaddamar da bincike kan faruwar lamarin.