Jami’ai sun kama wani manomin ganyen wiwi a Sokoto

Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA, ta sanar da kama wani da ake zargin manomin ganyen wiwi ne a jihar Sokoto.

Kwamandan hukumar ta NDLEA a jihar, Adamu Iro, ya shaida wa manema labarai a Sokoto a ranar Asabar cewa, “Wannan shi ne karo na farko da irin wannan lamari ya faru a tarihin jihar.”

Mista Iro ya ce an kama wanda ake zargin Anas Sani ne a kauyen Sayinna da ke karamar hukumar Tambuwal, bayan da aka samu labari.

Ya ce wanda ake zargin ya shuka wata irin tabar wiwi na kasar waje a gonarsa ta masara, wadda jami’an NDLEA suka gano.

A cewarsa, za a gurfanar da wanda ake zargin bayan binciken kimiyya na ganyen da aka tumbuke.

More News

Ƴansanda sun hallaka masu garkuwa da mutane

Ƴansanda sun hallaka wasu masu garkuwa da mutane uku da ake zargin sun yi yunkurin yin garkuwa da matar wani dan majalisar dokokin jihar...

Ƴansanda a Katsina sun yi nasarar cafke wasu tantiran masu safarar alburusai wa ƴanbindiga

Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina a ranar Juma’a ta sanar da cewa ta kama wasu manyan ‘yan bindiga guda uku tare da kwato manyan...

Tinubu ya amince da mafi karancin albashi na N70,000

Shugaba Bola Tinubu ya amince da N70,000 a matsayin mafi karancin albashi ga ma’aikatan Najeriya, inda ya yi alkawarin sake duba dokar mafi karancin...

Mutanen Isra’ila sama da rabin miliyan sun tsere saboda yakin Gaza

Mutanen Isra'ila sama da rabin miliyan ɗaya ne suka fice daga ƙasar kuma ba su koma ba a watanni shida na farkon yaƙin Isra'ila...