Jaafar Jaafar: Babu hannun gwamnatin Kano

Abdullahi Umar Ganduje

Gwamnatin jihar Kano ta kalubalanci mawallafin jaridar Daily Nigeria da ake buga wa a Intanet kan zargin da ya yi cewa ana yi wa rayuwarsa barazana, saboda buga labarin zargin cewa gwamnan jihar yana karbar cin hanci.

Jaafar Jaafar ya bayyana wa BBC cewa ya shiga ‘yar buya tun bayan buga labarin cewa yana da wasu hotunan bidiyo da ke nuna gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje yana karbar cin hancin dala miliyan biyar daga ‘yan kwangila.

Tuni dai gwamnatin Kano ta yi watsi da zargin, inda ta ce an yi shi ne domin bata sunan gwamnan jihar saboda wata manufa ta siyasa, har ma tana duba yiwuwar daukan matakin shari’a.

A martanin da ya mayar kan zargin na baya-bayannan, babban mai taimaka wa Gwamna Abdullahi Ganduje kan kafofin sada zumunta Salihu Tanko Yakasai, ya ce babu kanshin gaskiya a kan cewa ana yi wa Ja’afar Ja’afar barazana.

Yace, “Magana da ake yi cewa Ja’afar Ja’afar rayuwarsa tana cikin barazana gaskiya abu ne da gwamnati ba ta san da shi ba, kuma ba ma ta da hannu a cikin wannan abin kwata-kwata”, in ji Salihu.

Ya kara da cewa idan har dan jaridar yana fuskantar barazana ya kamata ya kai rahoto ga jami’an tsoro domin su bincika su kuma ba shi kariya.

Salihu ya ce, “in dai da gaskiyar wannan magana to ya garzaya ya tafi wajen jami’an tsaro.”

Ya ce tuni gwamnati ta mayar da martani a rubuce kan zargin da jaridar ta buga, don haka ba ta bukatar mayar da martani ya hanyar barazana, abinda Salihu ya ce sam hakan ba halayyar gwamnatinsu ba ce.

More from this stream

Recomended