A kalla mutane 18 ne suka rasa rayukansu a wani mummunan haɗarin mota da ya faru a kan titin Ikorodu zuwa Sagamu, Jihar Ogun, a ranar Asabar da yamma.
Cikin waɗanda suka mutu har da wani jami’in Hukumar Kiyaye Haɗura ta Ƙasa (FRSC) daga ofishin Mosimi, wanda ya rasu yayin da yake aikin ceto.
Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 4 na yamma, inda motoci biyar da babura biyu suka yi taho-mu-gama.
Motocin da suka yi haɗarin sun haɗa da: motar Toyota Hiace mai lamba AGL752YC, manyan motocin DAF guda biyu – ɗaya na ɗauke da lamba T14007LA, ɗaya kuma babu lamba, motar Honda mai lamba HT680, wata mota kirar pickup mai lamba STF10204, da kuma baburan Bajaj biyu – ɗaya mai lamba AGG448Q, ɗaya kuma PKA214WS.
Mai magana da yawun hukumar, Florence Okpe, ta ce yayin da tawagar FRSC ke aikin ceto, wata mota da birkinta ya ƙi aiki ta afka musu, inda hakan ya yi sanadin mutuwar jami’in.
“Jami’an FRSC daga ofishin Mosimi sun fara aikin ceto ne bayan haɗarin da ya faru da misalin ƙarfe 4:00 na yamma, ranar Asabar, 5 ga Afrilu. Mutane 22 ne aka ruwaito sun shiga haɗarin – maza 14, mata 6, da yaro 1. Mutane huɗu sun jikkata, yayin da 18 suka mutu, ciki har da jami’inmu.”
Ta ce an garzaya da waɗanda suka jikkata zuwa Asibitin Dasochris da ke Gbaga, yayin da gawarwakin aka adana su a asibitin OOUTH.