Hatsari a ababen hawa ya fi kashe matasan Afirka fiye da HIV – WHO

A man attends to traffic in Zimbabwe

Hatsarin Mota ya fi kashe matasa a duniy

a.

Raunikan da ake samu a hatsarin ababen hawa sun fi kisan yara kanana da matasa a duniya, in ji wani rahoton hukumar lafiya ta duniya WHO.

Rahoton da hukumar ta wallafa ya nuna cewa a Afirka aka fi samun yawan mace-mace ta sanadiyar hatsarin ababen hawa a duniya.

Rahoton ya ce yawancin kasashen Afirka da na kasashen kudancin Amurka ba su da dokokin da ke takaita yawan gudun ababen hawa.

Hatsarin mota shi ne ya fi yawan kisan yara kanana da matasa ‘yan kasa da shekara 29, in ji rahoton.

Rahoton ya kara da cewa mutane sun fi mutuwa ta sanadiyar rauni a hatsarin mota fiye da cutar HIV da tarin fuka da kuma amai da gudawa.

“Wannan yawan mace-macen, adadi ne da ba za a amince da shi ba daga ababen hawa,” in ji Tedros Adhanom Ghebreyesus babban daraktan hukumar WHO.

Ya ce ba wani dalili na yin sakaci, domin matsala ce da za a iya maganinta.

‘Ba iyaka’

Rahoton WHO ya ce adadin yawan mace-macen da ake samu a Afirka ta sanadiyar hatsarin mota ya lunka wanda ake samu a nahiyar turai sau uku, yankin da ba a fiye samun matsalar ba.

Kusan rabin kasashen Afirka 54 ne ba su da dokar takaita gudu, a cewar rahoton.

Rahoton ya ce Botswana da Ivory Coast da Kamaru adadin ya fi karuwa, yayin da Masar da Angola da Burkina Faso da Burundi aka samu raguwar yawan matsalar mace-macen.

    Karuwan adadin mace-macen

    Alkalumman rahoton sun nuna kimanin mutum miliyan 1.35 hatsarin mota ya kashe a duniya a 2016, adadin da ya haura na shekarun baya.

    Hatsarin gamuwa da yawan hatsarin mota ya fi yawa a kananan kasashe.

    Yankin Kudancin Asiya ne na biyu bayan Afirka a yawan mace-mace ta sanadiyar hatsarin mota.

    More from this stream

    Recomended