A kalla mutane 10 ne suka rasa rayukansu a wani sabon hari da ‘yan bindiga suka kai a garuruwa biyar na Karamar Hukumar Bokkos da ke Jihar Filato.
Wannan hari ya zo ne kwanaki shida bayan irin sa da aka kai a Ruwi, inda aka kashe mutane 10 tare da jikkata wasu uku yayin da suke halartar jana’iza.
Shugaban Majalisar Raya Al’adu ta Bokkos (BCDC), Farmasum Fuddang, ya tabbatar da aukuwar lamarin a ranar Alhamis, yana mai cewa maharan sun fara kai hari a Mongor, amma jami’an tsaro sun fatattake su.
Bayan haka, suka koma garin Daffo, inda suka ci karo da martanin jami’an tsaro. Daga nan, suka sake kai hari a Manguna, Hurti da Tadai.
A cikin wata sanarwa da BCDC ta fitar, shugabanta ya bayyana cewa: “A cikin mako guda, mun rasa fiye da mutum 20 sakamakon wadannan hare-hare. Kawai a ranar 2 ga Afrilu, an kashe fiye da mutum 10. Muna gode wa sojoji da ‘yan sanda bisa gaggawar amsa kiranmu wanda ya taimaka wajen rage yawan asarar rayuka.”
Hare-haren ‘Yan Bindiga a Jihar Filato: Mutane 10 Sun Rasa Rayukansu
