Gwamnonin APC Sun Nemi Tinubu Ya Sake Tsayawa Takarar Shugaban Ƙasa a 2027

Gwamnonin da aka zaɓa ƙarƙashin jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya sun bayyana goyon bayansu ga shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu domin sake tsayawa takarar shugabancin ƙasa a zaɓen 2027.

Wannan mataki ya biyo bayan taron ƙoli na farko da jam’iyyar ta gudanar a yau.

Gwamnan jihar Imo kuma shugaban ƙungiyar gwamnonin jam’iyyar, Hope Uzodinma, ne ya fara gabatar da buƙatar a marawa shugaba Tinubu baya, inda gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani, ya goyi bayan buƙatar.

Daga bisani, an mika batun ga taron gaba ɗaya, inda yawancin mahalarta suka amince da shawarar.

Ko da yake shugaban ƙasa Tinubu bai shafe shekaru biyu a kan mulki ba, batun zaɓen 2027 ya riga ya fara ɗaukar hankali a harkokin siyasar ƙasar.

More from this stream

Recomended