Gwamnatin Tarayya za ta nome filayen manyan makarantu da ba a amfani da su

Gwamnatin tarayya ta bayyana wani shiri na amfani da filaye da ba a amfani da su a manyan makarantu domin noma a wani mataki na bunkasa samar da abinci a fadin ƙasar nan.

Ministan noma da samar da abinci Sanata Abubakar Kyari ne ya bayyana haka a cocin Seventh-day Adventist, yayin taron Eastern Nigeria Union Conference Centenary Public Lecture and Food mai taken ‘’ kawo karshen karancin abinci a Najeriya, yadda za a yi amfani da wanda ba a amfani da shi’ a Fatakwal ranar Juma’a.

Kyari, wanda ya samu wakilcin mataimakin daraktan kula da abinci na ma’aikatar, Nuhu Kilishi, ya ce tuni aka mika wa cibiyoyin wasiku, domin neman yardarsu.

Ya bayyana cewa wasu daga cikin manyan makarantun sun fara nuna yardarsu, yana mai cewa matakin zai zama tabbataccen mataki na farfado da noma a makarantu.

Kyari ya ce, “Muna son farfado da noma a makarantu da cibiyoyi. Mun rubuta wa jami’o’i da makarantu da su bar mu mu yi amfani da kadada na gonakinsu da ba a yi amfani da su ba.

More News

Ƴansanda sun hallaka masu garkuwa da mutane

Ƴansanda sun hallaka wasu masu garkuwa da mutane uku da ake zargin sun yi yunkurin yin garkuwa da matar wani dan majalisar dokokin jihar...

Ƴansanda a Katsina sun yi nasarar cafke wasu tantiran masu safarar alburusai wa ƴanbindiga

Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina a ranar Juma’a ta sanar da cewa ta kama wasu manyan ‘yan bindiga guda uku tare da kwato manyan...

Tinubu ya amince da mafi karancin albashi na N70,000

Shugaba Bola Tinubu ya amince da N70,000 a matsayin mafi karancin albashi ga ma’aikatan Najeriya, inda ya yi alkawarin sake duba dokar mafi karancin...

Mutanen Isra’ila sama da rabin miliyan sun tsere saboda yakin Gaza

Mutanen Isra'ila sama da rabin miliyan ɗaya ne suka fice daga ƙasar kuma ba su koma ba a watanni shida na farkon yaƙin Isra'ila...