Gwamnatin Tarayya ta musanta cewa tana shirin rusa gidaje 1,500 a unguwar Xhidu a Abuja

Gwamnatin Tarayya ta musanta rahotannin cewa tana shirin rusa gidaje 1,500 a yankin Xhidu da ke kusa da Lugbe Phase II a Abuja.

Shugaban sashen yada labarai na hukumar kula da gidaje ta tarayya, FHA Kenneth Chigelu ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa.

A makon da ya gabata ne dai aka yi ta yada cewa mazauna unguwar sun yi zargin cewa hukumar ta FHA ta shirya ruguza gidajensu domin wani estet da wani ɗan kasuwa mai zaman kansa zai gina.

A cewar mazauna yankin, matakin na FHA “ya keta haƙƙinsu na tsarin mulki a fili, yana watsi da jin daɗinsu a matsayinsu na ‘yan ƙasa, kuma yana zubar da mutuncin Najeriya a duniya.”

A halin da ake ciki, FHA ta ce ba ita ce ke da alhakin rusa ginin ba.

“Hukumar tana son gyara kuskuren tunanin da wasu manu neman filaye ke yi, wadanda a kullum suke yaudarar wasu ‘yan Najeriya da ba su ji ba ba su gani ba, ta hanyar karbar kudade daga hannunsu tare da sayar da filayen gwamnati.”

More News

Ƴansanda sun hallaka masu garkuwa da mutane

Ƴansanda sun hallaka wasu masu garkuwa da mutane uku da ake zargin sun yi yunkurin yin garkuwa da matar wani dan majalisar dokokin jihar...

Ƴansanda a Katsina sun yi nasarar cafke wasu tantiran masu safarar alburusai wa ƴanbindiga

Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina a ranar Juma’a ta sanar da cewa ta kama wasu manyan ‘yan bindiga guda uku tare da kwato manyan...

Tinubu ya amince da mafi karancin albashi na N70,000

Shugaba Bola Tinubu ya amince da N70,000 a matsayin mafi karancin albashi ga ma’aikatan Najeriya, inda ya yi alkawarin sake duba dokar mafi karancin...

Mutanen Isra’ila sama da rabin miliyan sun tsere saboda yakin Gaza

Mutanen Isra'ila sama da rabin miliyan ɗaya ne suka fice daga ƙasar kuma ba su koma ba a watanni shida na farkon yaƙin Isra'ila...