Gwamnatin tarayya ta bayyana shirinta na fara biyan bashin watanni tara ga masu cin gajiyar shirin N-Power da ke shirin farawa daga watan Nuwamba.
Ta bayyana hakan ne a ranar Litinin ta bakin Manajan shirye-shiryen N-Power na kasa, Akindele Egbuwalo, wanda ya bayyana hakan a wata ganawa da wasu masu cin gajiyar N-Power a ofishinsa da ke Abuja.
Egbuwalo a wata sanarwa da ma’aikatar kula da jin kai da yaki da fatara ta tarayya ta fitar, ya bayyana cewa babbar manufar dakatar da shirin na wucin gadi shi ne a magance duk wani abu da ya shafi masu cin gajiyar shirin kai tsaye.
A cikin sanarwar ya bayyana cewa, sakamakon dakatar da shirin na wucin gadi da aka yi na yin gyaran fuska da kuma binciken kwakwaf, an kwato kudade daga hannun wasu a ciki.