Gwamnatin Kano Ta Amince Da Biyan Bashin Albashin Ma’aikatan Tsabtace Muhalli Na Watanni Tara

Gwamnatin Jihar Kano, ƙarƙashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf, ta amince da biyan bashin albashin wata tara ga ma’aikatan tsabtace muhalli 2,369 a faɗin jihar.

Wannan biyan haƙƙin da ya shafi watannin Yuni 2024 zuwa Fabrairu 2025 an amince da shi ne domin tallafa wa ci gaban muhalli da kuma inganta jin daɗin ma’aikatan.

Da yake bayyana wannan ci gaba, Kwamishinan Muhalli da Sauyin Yanayi, Dakta Dahir M. Hashim, ya jaddada cewa gwamnatin na da ƙudirin inganta rayuwar al’umma da kuma tabbatar da tsaftar muhalli.

“Biyan waɗannan bashin albashi a kan kari zai ƙara ƙwarin gwiwa ga ma’aikatan tsabtace muhalli, waɗanda suka nuna ƙwazo duk da jinkirin da aka samu,” in ji Dakta Hashim.

Ya jinjinawa ma’aikatan bisa haƙuri da juriya da suka nuna, yana mai yabawa da rawar da suke takawa wajen tabbatar da tsaftar muhalli a jihar.

Haka nan, Dakta Hashim ya bayyana cewa wasu ma’aikatan tsabtace muhalli, ciki har da masu duba gidaje da kuma membobin ƙungiyar Sanitation Vanguard, suma za a tantance su don samun irin wannan biyan. Ma’aikatar ta bukaci waɗanda abin ya shafa su shirya don tantancewa nan gaba.

More from this stream

Recomended