Gwamnatin Abia za ta fara biyan albashi mafi maranci na naira 70,000 a watan Oktoba

Gwamnatin Jihar Abia ta sanar da cewa za ta fara biyan sabon albashi mafi karanci na naira 70,000 ga ma’aikatanta daga watan Oktoba 2024.

Kwamishinan Watsa Labarai, Yarima Okey Kanu, ya bayyana wannan bayani ranar Talata yayin da yake zantawa da manema labarai kan sakamakon taron majalisar zartarwa ta jiha da aka gudanar a ranar Litinin karkashin jagorancin Gwamna Alex Otti.

“Gwamnatin jiha na da cikakken aniyar biyan albashin mafi karanci, kuma saboda haka, a cikin ‘yan kwanaki masu zuwa, za a fara biyan wannan albashi,” inji Kanu.

Kwamishinan Kwadago da Samar da Ayyuka, Sunny Onwuma, ya sake tabbatar da kudurin gwamnatin jihar na biyan albashin mafi karanci na kasa na naira 70,000.

Haka kuma, Kanu ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta amince da sabon aikin gina hanyoyi guda tara a fadin mazabun sanatoci uku na jihar.

More from this stream

Recomended