Gwamnati za ta fara biyan ma’aikata naira 30,000 mafi ƙarancin albashi a Zamfara


Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal Dare ya sanar da cewa za su fara aiwatar da tsarin mafi ƙarancin albashi naira 30,000 ga ma’aikatan jihar daga farkon watan Yuni mai zuwa.

Gwamnan ya faɗi hakan ne a wata ganawa da ya yi da shugabannin ƙungiyar ƴan ƙwadago reshen jihar.

Tun da farko dai ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa reshen jihar Zamfara ta bai wa gwamnatin jihar wa’adi zuwa ranar 23 ga watan Mayu ta fara aiwatar da mafi ƙarancin albashin, tare da barazanar shiga yajin aiki matuƙar aka gaza cimma matsaya.

More from this stream

Recomended