Gwamna Uba Sani Ya Nada Sarkin Kauru A Matsayin Amirul Hajj

Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya nada Mai Martaba Sarkin Kauru, Alhaji Ya’u Shehu Usman, a matsayin Amirul Hajj da jagoran tawagar gwamnatin jihar don aikin Hajjin 2025.

A cikin wata sanarwa da Kakakin Yada Labaran Gwamnan, Ibraheem Musa, ya fitar, an bayyana cewa an zabi Sarkin ne bisa la’akari da jajircewarsa, rikon amana, da kuma iya tafiyar da al’amuran jama’a cikin nasara.

Sanarwar ta kara da cewa Amirul Hajj zai yi aiki kafada da kafada da Kwamitin Hajj na Musamman na Kaduna da sauran hukumomi a matakin jiha, tarayya, da na kasa da kasa domin tabbatar da ingantaccen aikin Hajjin bana.

Gwamna Uba Sani ya taya sabon Amirul Hajj murna, yana mai bukatar ya yi amfani da kwarewarsa da basirar shugabanci wajen sauke nauyin da aka dora masa. Haka kuma, ya roki Allah ya ba shi jagora da kariya a wannan sabon aiki.

More from this stream

Recomended