Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya tabbatar da kama mutum 22 da ake zargi da hannu a kisan wasu mutane 12 ‘yan asalin jihar Kaduna da aka kashe a jihar Filato.
Rahotonni sun bayyana cewa waɗanda abin ya shafa na kan hanyarsu ce zuwa bikin aure da za a yi a Quan Pan, daga Kaduna, yayin da aka tare su a karamar hukumar Mangu ta jihar Filato a ranar Asabar da ta gabata, inda aka yi musu kisan gilla.
Da yake jawabi yayin da ya kai ziyara ga waɗanda suka jikkata a harin, wadanda ke karɓar magani a asibitin 44 Nigerian Army Reference Hospital da ke Kaduna, Gwamna Sani ya bayyana harin a matsayin “na mahaukaci ne kuma abin ƙyama.”
Ya ce yana ci gaba da tattaunawa da Gwamnan Filato, Caleb Mutfwang, da kuma Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu domin ganin an hukunta waɗanda ke da hannu a wannan ta’asa.
“Na yi kira da kira ga hukumomin tsaro su kama duk masu hannu a wannan al’amari, kuma yanzu an kama mutum 22 da ake zargi,” in ji Sani.
Gwamnan ya jinjina wa al’ummar Kaduna bisa yadda suka zauna lafiya duk da wannan mummunan abu da ya faru. Ya kuma roƙi shugabannin al’umma su ci gaba da wayar da kan jama’a don guje wa tashin hankali da ɗaukar fansa.
A ƙarshe, Gwamna Sani ya sake jaddada aniyar gwamnatinsa ta yin aiki da hukumomin tsaro domin tabbatar da adalci ga waɗanda aka kashe da kuma kare rayuka da dukiyoyin jama’a a gaba.
Gwamna Uba Sani: An Kama Mutum 22 Kan Kisan Mutanen Kaduna a Filato
