Gwamna da minista sun mutu a hatsarin jirgi a Sudan

Map

Jirgin sama mai saukar angulu ya yi hatsari a gabashin Sudan, inda ya kashe gwamna da wasu jami’ai hudu.

Rahotanni sun ce jirgin ya kama da wuta ne bayan da ya daki wani ginin filin jirgi a yayin da yake kokarin sauka a jihar Al Qadarif.

Amma babu tabbaci daga hukumomin kasar kan dalilin da ya janyo hatsarin jirgin.

Gwamnan jihar Qadarif ne Mirghani Salih ya rasa ransa a hatsarin, da kuma wasu akalla mutum hudu da suka hada da da minista da jami’an tsaro.

Yawancin jiragen sojin Sudan ta sayo su ne daga tsohuwar daular Soviet.

A watan Oktoba akalla mutum takwas suka samu rauni bayan wasu jiragen soji biyu sun yi taho-mu-gama a Khartoum babban birnin kasar.

More from this stream

Recomended