Gwamna Bala Ya Kori Akawun Jami’ar Sa’adu Zungur Kan Zargin Rashin Gaskiya da Cin Hanci

Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed, ya kori Ayuba Mohammed Gital daga mukaminsa na Akawun rikon kwarya na Jami’ar Sa’adu Zungur (SAZU) saboda zargin almundahana da rashin gaskiya wajen tafiyar da kudaden jami’ar.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Talata yayin da yake karɓar rahoton kwamitin da aka tura domin binciken harkokin gudanarwa da kudi na jami’ar. Ya ce ya damu matuka da yadda ake tafiyar da kudade tun kafuwar jami’ar a shekarar 2012.

Sanata Bala ya kuma bayyana cewa gwamnati za ta kafa kwamitin duba lissafi domin binciken yadda ake kashe kudaden da jami’ar ke samu daga ɗalibai da sauran hanyoyin samun kudi.

Shugabar kwamitin binciken, Farfesa Gambo Laraba Abdullahi, ta bayyana cewa sun kai ziyara dukkan sassan jami’ar kuma sun tattara bayanai daga takardun koke-koke guda 47 da suka haɗa da na kungiyar malaman jami’o’i (ASUU), inda suka bayyana matsalolin da suka shafi kudade da gudanarwa.

Farfesa Abdullahi ta ƙara da cewa an ƙara adadin kudin da ake ware wa jami’ar zuwa Naira miliyan 400 a kowane wata, inda ta shawarci gwamnati da ta sake nazarin tsarin raba jami’ar zuwa sansanonin karatu da dama.

More from this stream

Recomended